Amirka na buƙatar a tsagaita wuta a Siriya | Labarai | DW | 11.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka na buƙatar a tsagaita wuta a Siriya

Ministocin harkokin waje na ƙasashen da ke da hannu a yaƙin da ake yi a Siriya sun soma gudanar da wani taron na samar da hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin Siriya.

Münchener Sicherheitskonferenz 2015 Kerry Ankunft

John Kerry ministan harkokin wajen Amirka

Taron wanda ke gudana a birnin Munich da ke a nan kudancin Jamus ana sa ran Amirka da sauran ƙawayenta za su samu damar yin ƙarin matsin lamba ga Rasha da ta tsagaita wuta.

Tun farko gwamnatin Rasha da ke goyan bayan gwamnatin Bashar Al Assad ta yi furcin cewar a shirye take ta dakatar da bude wuta,to amma Amirka ta ce ta na buƙatar a dakatar da buɗe wutan nan take.