1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin samun 'yancin kai a Amirka

July 3, 2020

Kasar Amirka na bikin samun 'yancin cin gashin kai daga Turawan Ingila, a daidai lokacin da take fuskantar kalubalen annobar coronavirus da yakin zabe mai cike da rudani da kuma zanga-zangar blacklivesmatter.

https://p.dw.com/p/3el8w
Donald Trump da maidakinsa Lady Melania a bukukuwan samun 'yancin kai na Amirka
Donald Trump da maidakinsa Lady Melania a bukukuwan samun 'yancin kai na AmirkaHoto: Getty Images/AFP/S. Loeb

A ranar hudu ga wannan wata na Yuli da muke ciki ne dai, Amirkan ke cika shekaru 244 da samun 'yancin kanta. A shekara ta 1776 ne dai Amirkan ta samu 'yancin cin gashin kan nata daga Turawan Ingila. Bisa al'ada a irin wannan rana, shugabanni da talakawa sukan yi jawabai da tarurruka da ziyarce-ziyarce da wasan kyastun wuta da a kan yi a kusan kowanne gari. Sai dai matsalolin annobar cutar coronavirus da ta janyo hana cunkoson jama'a, kusan a iya cewa ta kawo nakasu ga wadannan shagulgula.

Miliyoyin mutane dai sun rasa ayyukansu a kasar, ta daya gefe kuma hankula sun karkata ga babban zaben shugaban kasa da ke tafe a cikin watan Nuwamba mai zuwa. Yayin da wasu bakar fatar Amirkan suke yin koyi da ra'ayin tsohon dan gwagwarmaya Fredrick Douglos, wanda tun kusan shekaru 80 da suka wuce ya gwasale irin wannan rana da yin korafin cewa rana ce ta jar fata, musanman ganin cewa 'yancin da wasu ke babatu kansa, suna ne ga bakar fata.