1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: An fara siyar da maganin zubar da ciki

March 2, 2024

Manyan kamfanonin hada magunguna na CVS da Walgreens a Amirka sun sanar da fara siyar da maganin zubar da ciki na mifepristone da takardar shaida daga likita.

https://p.dw.com/p/4d6AT
Kamfanonin CVS da Walgreens a Amirka sun fara siyar da maganin zubar da ciki na mifepristone
Kamfanonin CVS da Walgreens a Amirka sun fara siyar da maganin zubar da ciki na mifepristoneHoto: Jimin Kim/SOPA/Sipa/picture alliance

Kamfanonin guda biyu sun ce za su fara siyar da maganin ne a jihohin New York da Pennslvania da Califonia da kuma sauran wasu jihohin da aka amince da zubar da ciki.

A watan Janairun bara ne dai, hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar ta kaddamar da wata doka da za ta bada damar samun maganin na mifepriston da kuma fadada samar da shi a manyan shagunan siyar da magunguna na kasar.

Shugaban kasar Amirka Joe Biden ya yi maraba da wannan matakin, inda a cewarsa wannan ci gaba ne ga masu muradun yin hakan