1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kace-nace kan hana zubar da ciki a Amirka

Mouhamadou Awal Balarabe
June 24, 2022

Wasu jihohin Amirka sun sanar da fara daukar matakan hana zubar da ciki don radin kai, sakamakon hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na soke 'yancin zubar da ciki.

https://p.dw.com/p/4DDfq
Symbolbild I Pro-Abtreibung
Hoto: Sachelle Babbar/ZUMA/picture alliance

Babban mai shigar da kara na Missouri ya sanar cewa jihar ta tsakiyar Amirka ta zama farko da ta hana zubar da ciki. Shi ma gwamnan jihar Dakota ta Kudu na jam'iyyar Republican Kristi Noem, ya sanar da cewa, daga yanzu zubar da ciki ya sabawa doka a wannan jiha ta Arewacin Amirka.

Sai dai a lokacin da yake tsokaci kan wannan batu, shugaban Amirka Joe Biden ya ce hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na soke hakkin zubar da ciki wani "kuskure ne mai ban tausayi" sakamakon "akidar tsattsauran ra'ayi". A na shi bangaren tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya ce mutunta "nufin Allah" ne.