Amirka: Hukuncin kotu kan dokar baki | Labarai | DW | 10.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka: Hukuncin kotu kan dokar baki

Wata kotun daukaka kara ta Amirka da ke San Francisco ta yi watsi da bukatar shugaba Donald Trump da ke neman gwamnatinsa haramtawa wasu kasashen musulmi bakwai shiga kasar.

A wani zama da ta yi, kotun mai alkalai uku ta ce bangaren Trump bai gabatar da wata hujja mai gamsarwa ba da zai sa a cigaba da aiwatar da wannan doka ta hana baki daga kasashen Somalia da Yemen da Syria da Iran da Iraqi da Sudan da kuma Libya shiga kasar ta Amirka ba. Kotun ta yi nuni da cewa akwai bukatar al'ummar Amirka su mutunta dokar kasa ciki har da shugaba, to sai dai tuni Shugaba Trump ya wallafa a shafin sa na Twitter cewa akwai kotu na gaba wanda hakan ke nuni da cewar zai daukaka kara inda a share guda ya ce wajibi a dau matakan tsare kasa.