Amirka: Fiye da mutun dubu 100 sun mutu da corona | Labarai | DW | 28.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka: Fiye da mutun dubu 100 sun mutu da corona

Kasar Amirka ta zarta adadin mutun dubu 100 da suka mutu bisa kamuwarsu da cutar Covid-19, a yayin da Brazil ta haura adadin mutun dubu 25 da suka mutu, lamarin da ya kara adadin mamata dubu 350 a duniya.

Wannan lamarin na zuwa ne a yayin da kasashen duniya ke ci gaba da yin sakin mara ga matakan takaita zirga-zirgar jama'a da suke dauka don dakilye yaduwar cutar, inda tuni jihohin  Las Vegas da birnin Washington suka ambata sake bude wasu harkokin yau da kullun ciki har da gidajen cin abinci kama daga farkon watan gobe, a yayin da Rasha ke shirin soma fita daga dokar kulle a ranar Litinin din makon gobe.