Amirka: Dokar yi wa hajojin Chaina karin haraji ya soma aiki | Labarai | DW | 10.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka: Dokar yi wa hajojin Chaina karin haraji ya soma aiki

Chaina ta ce za ta dauki mataki daidai da wanda Amirka ta dauka na lafta wa kayayyakin kasar da ke shiga Amirkan karin haraji bayan da Amirka ta ce a hukumance dokar ta soma aiki a wannan Juma'a.

A wannan Juma'ar Amirkan ta sanar da wannan mataki na yin kari daga kashi goma zuwa kashi ashirin da biyar cikin dari kan duk hajoji na Chaina da za su shiga kasar. Tun a watan Disambar bara, kasashen biyu suke tattaunawa,  a kokarin da suke na kawo karshen sabanin kasuwancin da ke tsakaninsu wanda ya ke kuma cutar da tattalin arzikin duniya.