Amirka da Taliban sun yi musayar fursunoni | Labarai | DW | 01.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka da Taliban sun yi musayar fursunoni

Hukumomin Amirka sun tabbatar da cewa an sako wani sojansu da aka sace shekaru biyar a Afganistan, inda Amirka kuma ta sako 'yan Taliban biyar.

Wannan musayar fursononin tsakanin mayakan Taliban da gwamnatin Amirka, kasar Qatar ce ta jagoranci aka yi shi. Kungiyar Taliban a Afganistan ta saki wani sojan Amirka da ta kama shekaru biyar da suka gabata, yayin da ita kuwa Amirka ta saki wasu 'yan Taliban biyar da suke tsare a gidan yarin Guantanamo. Sojan na Amirka da aka sako Sergeant Bowe Bergdahl, a yanzu haka an kawo shi kasar Jamus domin duba lafiyarsa, a wani sansanin sojojin Amirka da ke kasar ta Jamus.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasir Awal