1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta sanyawa Iran takunkumai na tattalin arziki

Ramatu Garba Baba
November 2, 2018

Gwamnatin shugaba Trump ta cika alkawarinta na sanyawa Iran takunkumi da zai soma aiki daga ranar Litinin mai zuwa bayan da ta soke yarjejeniyar nukiliyar da kasashen duniya suka kulla da ita kan shirinta na nukiliya.

https://p.dw.com/p/37asC
USA Bedminster Donald Trump unterzeichnet Iran Sanktionen
Hoto: Shealah Craighead

Sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, ya ce an dauki matakin don ladabtar da kasar, ya kuma lissafo wasu bukatu da ya ce, dole Iran ta cika in har tana so a janye takunkumin, ciki Amirka ta nemi Iran ta janye goyon bayan da ta ke bai wa wanzuwar ayyukan ta'addanci tare da dakatar da shirin nukiliyarta.