Amirka: An janye haramci shiga ga 'yan Chadi
April 11, 2018Talla
Shugaba Donald Trump a ranar Talata ya janye sanya takunkumi na hana al'ummar kasar Chadi ziyartar kasar Amirka abin da ke zuwa bayan watanni ana nazarin kasar.
Kamar yadda fadar White House ta bayyana kasar da ke a Tsakiyar Afirka ta inganta harkoki na tsaronta, ta kuma kara yawan musayar bayanai da take yi da Amirka kan abin da ya shafi al'ummarta.
Kasar ta Chadi dai ta kasance cikin kasashe takwas da Amirka ta sanya masu takunkumi na hana shigar al'ummarsu kasarta, kasashen da suka hadar da Iran da Libiya da Siriya da Somaliya da Yemen da Banizuwela da Koriya ta Arewa. Kasar ta Chadi dai ana kallonta a matsayin muhimmiyar kasa ga Amirka a fagen yakin da take yi da ta'addanci.