Amincewa da karin wa′adin da aka ba Girka | Labarai | DW | 27.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amincewa da karin wa'adin da aka ba Girka

Majalisar dokokin Jamus ta amince da tsawaita wa'adi da aka yi wa Girka na biyan basuka da aka ba ta don farfado da tattalin arzikinta da ya shiga halin ni 'yasu.

Majalisar dokokin Jamus ta amince da tsawaita wa'adin da aka baiwa kasar Girka na watanni hudu don samun sukunin biyan basukan da aka bata da nufin ceto tattalin arzikinta da ya kama hanyar durkushewa.

'Yan majalisu 541 daga cikin 586, su ne dai suka goyi bayan tsawaita wa'adin zuwa watan Yunin bana a zaman da majalisar ta yi a yau Juma'a.

Akwai dai daga cikin bangarorinn da ba su amince hakan ba, dama wasu daga cikin 'yan majalisar da ba su sami zaman na yau ba, kamar yadda rahotannin da suka fito daga zaman suka nunar.