Amfani da Nau’ra mai ƙwaƙwalwa da Amfani da fasahar yanar Gizo a Afirka | Learning by Ear | DW | 16.04.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

Amfani da Nau’ra mai ƙwaƙwalwa da Amfani da fasahar yanar Gizo a Afirka

default

Amfani da Nau’ra Mai ƙwaƙwalwa da Amfani da Fasahar Yanar Gizo a Afirka.

Amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa domin neman ilimi da wasu bayanai ya zama ruwan dare a ƙasashemmu na Afirka, saboda yanzu kusan ko’ina ka duba za ka ga cewa ana amfani da nau’ra saboda ana iya samun nau’ra akan Kuɗi ƙalilan.

Shirin Ji Ka Ƙaru zai koyar da duk mai so yadda za a yi amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa domin ‘yan boko da ma duk wanda ke buƙata ya yi bincike ko wani nazari akan abin da ya shafi duniyar mu a yau.

Kamar yadda muka faɗa a baya can, amfani da nau’ra mai ƙwaƙwalwa ko yanar gizo, ya zama ruwan dare, saboda inda duk ka duba kama daga ofisoshi, jami’o’i da makarantun kimiya da fasaha, duk suna amfani ne da yanar gizo wajen koyar da dalibai, a taƙaice dai ana cewa duniya ta kasance a tafin hannunka, kana gida ko makaranta za ka iya yin karatunka ba sai ka fita zuwa wata ƙasa ba.

Sanin aiki da na’ura

Shirin Ji Ka Ƙaru zai fayyace yadda ake amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa ta yadda za ka nemi abokai ko kuma wani bincike na musamman.

An yi shirin na Ji ka ƙaru a harsuna shidda, waɗanda suka haɗa da Ingilishi, Kiswahili, Faransanci, Hausa, Portuguese, da Amharic.

Shirin Ji Ka Ƙaru na samun gudunmuwa ne daga ofishin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Jamus.

Sauti da bidiyo akan labarin