1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Bikin ranar mata ta duniya

Mohammad Nasiru Awal RGB
March 8, 2021

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na daga cikin kasashen duniya da ake amfani da cin zarafin mata a matsayin makamin yaki. A shekarar da ta gabata mata na daga cikin wadanda aka tilasta wa shiga aikin sojojin sa-kai.

https://p.dw.com/p/3qMaJ
Symbolbild - Frauenrechte in Pakistan
Gangamin mata don hana cin zarafinsuHoto: Getty Images/AFP/A. Ali

Albarkacin ranar mata ta duniya, tashar DW ta zanta da wata mace soja, wadda bisa dalilin cin zarafinta da aka yi, ta yanke shawarar daukar makami a hannu. Mama Faida kamar yadda 'yan uwanta sojojin sa-kai ke kiranta, uwa ce mai 'ya'ya shida. Kimanin shekaru 17 da suka gabata ta shiga kungiyar masu daukar makami. Dalilin yin haka kuwa shi ne wani abin da ya faru da ita da ba za ta taba mantawa ba. A lokacin, tana da shekara goma sha biyar da haihuwa, tana aiki a gonar mahaifinta, wasu maza rike da adduna suka kashe mahaifinta, suka yi awon gaba da ita, Faida ta ce "Na ga yadda mayakan Kungiyar FDLRsuka kashe mahaifina da dukkan 'yan uwa da dangina. Ba zan iya ci gaba da rayuwa a haka ba. Saboda haka na yanke shawarar daukar makami na shiga soja don in fatattake su." Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango dai ta yi kaurin suna wajen yi wa mata fyade. 

Südafrika Aufruhr wegen sexuellen Missbrauchs in Diepsloot
Matsalar fyade ta yi kamari a KwangoHoto: Reuters
Yadda wasu mata ke karbar horo don kare kansu daga fyade
Yadda wasu mata ke karbar horo don kare kansu daga fyadeHoto: Africa Yoga Project

Kungiyoyin agaji sun kiyasta yawan wadanda suka tsira daga ukubar fyade da mutum fiye da dubu dari biyu. Sojojin sa-kai na yi wa mata da maza da kanana yara fyade da nufin sanya tsoro a zukatan al'umma su kuma fatattake su daga yankuna masu arzikin karkashin kasa da kuma gonakinsu. Ana amfani da cin zarafin mata ta hanyar lalata a matsayin wani makami na yaki. Wadanda suka tsira kamar Mama Faida na bukatar tsawon shekaru kafin su farfado daga cin zarafin da aka yi musu. Faida na ci gaba da jimamin rashin mijinta.  Karin Bayani: Ranar yaki da kaciyar mata

Bayan an kashe mijinta an kuma yi mata fyade, iyalanta da kawayenta sun juya mata ba. Ta shiga ukuba a rayuwa, ta sha gwagwarmayar kula da da 'ya'yanta, har zuwa lokacin da tsohon malaminta da take kira Janar Mbura daga birnin Goma ya zo kauyensu don wayar da jama'a kai, yana kuma neman wadanda za su shiga yaki don fatattakar 'yan kungiyar FDLR. Daga cikin wadanda suka amsa kiransa har da Faida. Yanzu dai Faida ta sadaukar da dukkan karfinta wajen kula da 'ya'yanta, tana kuma fata za su yi rayuwa da babu tashin hankali a cikinta "Da yardar Ubangiji, zan ba su ilimi ina kuma fatan ilimin zai yi albarka. Ba ni da wani aiki dabam da nake yi, ba zan iya duba su ni kaidai ba sai da taimako." Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa a bara akalla mutum dubu biyu sojojin sa kai masu daukar makamai suka kashe a larduna uku na gabashin Kwango, sannan an tilasta wa fiye da miliyan biyar da dari biyar tserewa daga gidajensu. Kwango na da yawan 'yan gudun hijira na cikin gida fiye da kowacce kasa a Afirka.