1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yancin mata da daidaituwar al'amura

Lateefa Mustapha Ja'afar MNA
March 11, 2019

Ranar Mata Ta Duniya: Batun na 'yancin mata shi ne abin da shirin na wannan lokaci zai mayar da hankali a kai.

https://p.dw.com/p/3EnDt
Türkei Weltfrauentag in Istanbul - Protest
Hoto: Reuters/M. Sezer

Shirin na wannan lokaci zai yi nazari ne kan ranar mata ta duniya, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware kuma ake gudanar da bikin a ranar takwas ga watan Maris na kowacce shekera. Shirin dai ya ji ta bakin matan su da kansu da kuma kungiyoyin da ke rajin kare hakkin mata. Taken bikin na wannan shekarar dai shi ne "Daidato domin samun ci-gaba".

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, shin me kungiyoyin da ke rajin kare hakkin mata ke yi domin wayar da kan matan kan hakokinsu da kuma 'yancin da suke da shi?

Shin su kansu matan sun san cewa akwai wata rana da Majalisar Dinkin Duniya ta ware da zummar yin bukukuwa domin 'yancinsu?

Wadannan tambayoyi ne dai shirin na wannan lokaci zai amsa.