1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ta kashe mutane sama da 100

September 4, 2022

Rahotannin daga kasar Sudan na nuni da cewa daga watan Mayu, fiye da mutane 100 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu dubbai suka rasa matsugunnansu sanadiyar ambaliyar ruwa.

https://p.dw.com/p/4GPGw
Flood in Sudan
Hoto: Sami Alopap/AA/picture alliance

Kasar dai ta sha fama da ifta'i na ambaliyar daga watan Mayu zuwa watan Agusta kowace shekara wanda ke haifar mata da dimbin asara. 

Alkalumman Majalisar dinkin Duniya sun yi nuni da cewa ambaliyar ruwan ta shafi fiye da mutane 2,200. Majalisar Dinkin Duniya ta kuma yi gargadin cewa ta yiwu alkalumma wandanda ambaliyar za ta shafa su nunku fiye da shekarar bara.

Ifta'in na bana dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin dambarwar siyasa da na tattalin arziki da ya ta'azzara sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a bara karkashin jagorancin Hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan.