1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan na bukatar agajin gaggawa

Ramatu Garba Baba MAB
August 28, 2022

Gwamnatin Pakistan ta nemi taimakon kasashen duniya a sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyar rayukan mutum fiye da dubu daya.

https://p.dw.com/p/4G9Co
Pakistan - Flut
Hoto: Asif Hassan/AFP

Yawan mutanen da ambaliyar ruwa ta halaka a kasar Pakistan sun haura dubu daya kamar yadda alkaluman da mahukuntan kasar suka fitar a wannan Lahadin ya nunar. Tuni gwamnatin kasar ta ayyana dokar ta baci a yayin da Firaiminista Shahbaz Sharif ya yi kira ga manyan kasashen duniya don kawo wa kasar dauki.

Mutum sama da miliyan talatin daga cikin al'ummar kasar na cikin yanayi na bukatar taimako a sakamakon bala'in ambaliyar ruwa da akasarin 'yan kasar suka ce ba su taba ganin irinsa ba duk da cewa ambaliya ba sabon abu bane a kasar, amma ruwan a bana ya sauka ninkin ba ninkin yadda aka saba gani a cikin watan Augustan kowacce shekara a Pakistan.