1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa a Afrika.

Yahouza S.MadobiSeptember 19, 2007

A ƙasashe da dama na Afrika, ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar jama´a tare da hadasa asara dukiyoyi masu yawa

https://p.dw.com/p/BtuZ
Hoto: AP

Ƙurraru ta fannin hasashen sararin samaniya, sun hango ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da za su zuba, tsakanin 18 zuwa 24 ga watan da mu ke ciki a yankin yammacin Afrika.

A game da haka, hukumar Majalisar Ɗinkin Dunia, mai kulla da bada agajin gaggawa, ta nuna damuwa, ta la´akari da halin da milion jama´ar wannan yanki ke ciki, a sakamakon ambaliyar ruwan da su ka gabata.

Ƙiddidigar da hukumar ta Majalisar Ɗinkin Dunia mai kulla da baga agajin gaggawa wato OCHA, ta gano cewar a ƙalla mutane 270 su ka rasa rayuka, sannan mutane milion 1, su ka rasa matsugunai a faɗin Afrika ta yamma a sakamakon ambaliyar ruwa da ta rutsa da su, a damar shekara bana.

A cewar shugabar hukamar ta OCHA, ya zuwa yanzu sun duƙufa wajen kai agaji ga wannan jama´a, tare da taimakon ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.

A game da haka, ƙungiyar bada tallafi ta Care International, hukumar abinci ta Majalisar Ɗinkin Dunia, da Red Cross sun bada taimako mai tsoka domin samar da abinci ga wanda bayin Allah da kuma gina masu matsugunan wucin gadi.

A wata sanarwa da ta fiddo yammacin jiya gwamnatin ƙasar Jamus ta alƙawarta ƙarin taimako na Euro dubu 430.

ƙungiyoyin bada agaji za su aanfani da wannan kuɗi domin sayen barguna da gidajen sabro ga jama´ar da ambaliyar ta rutsa da su.

Cemma a makon da ya gabata, gwamnatin Jamus ta bada Euro dubu 130 ga ƙasashen Ghana da Sudan

Wannan itace ambaliyar ruwa mafi muni da Afrika ta fuskanta tun tsawan shekaru 30 da su ka gabata.

Ƙasar Sudan ke sahun gaba ta fannin asara rayuka, tare da mutane 64,sannan sai Ghana, wada ta yi asara mutane 32 a cewar Majalisar Ɗinkin Dunia.

A Tarayya Nigeria, rahottani sun nunar da cewa, mutane 41 sun rasa rayuka, 22 a Burkina Faso, 20 a Togo, 18 a Ruwanda ,kimanin 10 a Jamhuriya Niger.

Kazalika, ambaliyar ta shafi ƙasashen Mauritania Marroko Somalia Ethiopia da Uganda.

A cewar shugabar hukumar OCHA,Elisabeth Byrs,a halin yanzu ana fuskantar ɓullar cuttutuka da dama, a matsugunnan yan gudun hijira da ruwan ya kora daga gidajen su.