Ambaliya za ta yi muni a Amirka | Labarai | DW | 28.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliya za ta yi muni a Amirka

Hukumar da ke kula da yanayi ta Amirka, ta ce lamura na iya kazanta a biranen Houston da kuma Texas wadanda ke cikin wani ibtila'in ambaliyar ruwa.

USA Unwetter Harvey (Getty Images/J. Raedle)

Mazauna Houston da ke fama da ambaliya

Hukumar da ke kula da yanayi ta Amirka, ta ce lamura na iya kazanta a biranen Houston da kuma Texas wadanda ke cikin wani ibtila'in ambaliyar ruwa. Kamar yadda hukumar ta hasaso, akwai yiwuwar samun ruwan sama mai yawan gaske cikin 'yan kwanakin da ke tafe in da zai fi shafar wurare irinsu Lake Charles da Louisiana da kewaye. Akalla mutane dubu 45 ne ke cikin matukar bukatar dauki a Texas, inda gwamnati ta ce ta shirya samar da wuraren fakewa ta wucin-gadi ga akalla dubu 30.