1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliya ta yi barna a Chadi

Usman Shehu Usman
August 15, 2024

Akalla mutane 54 suka mutu a kasar Chadi sakamakon ambaliyar ruwa inda kuma wasu mutanen da yawa suka suka bace bayan an dauki kusan sati guda ana ruwan sama ba kakkautawa

https://p.dw.com/p/4jWfp
Überschwemmung  Daressalam Tansania
Hoto: Amas Eric/DW

A cewar hukumomin kasar Chadi, ambaliyar ta biyo bayan ruwan sama da aka fara yi tun Juma'ar da ta gabata har izuwa jiya Laraba . Rahotanni suka ce ruwan da ya malala baya ga rayukan mutane 54 ya kuma share gidaje da yawa da kuma shaguna musamman a arewacin kasar ta Chadi. Shugaban ma'aikatar lura da yanayin kasar Idriss Abdallah Hassan, ya fada wa manama labarai cewa wannan ambaliyar ruwan ta shafi sauyin yanayi ne, wanda kuma ke faruwa kusan duk bayan shekaru biyar ko goma. Akasarin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar hadi da wadanda yanzu suka bace ana nemansu, baki 'yan ci-rani ne da ke aikin hako ma'adinai a lardin arewacin Chadi can kusa da iyakarsu da kasar Libiya.