1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Ambaliya ta kashe mutane 41 a Angola

Mouhamadou Awal Balarabe
January 9, 2020

An shafe sa'o'i da dama ana ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohi da dama na Angola, lamarin da ya jawo ambaliya tare da haddasa asarar kadarori da rayukan mutane da dama a kudacin kasar.

https://p.dw.com/p/3VxXw
Angola Überschwemmungen in Kwanza Norte
Hoto: DW/A. Domingos

Mutane 41 sun mutu a Angola sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe kusa kwana guda ana shararawa a akasarin garuruwa na kasar.  A wani taron manema labarai da ya gudanar a Luanda babban birnin Angola, ministan Cikin gida Eugenio Laboinho ya ce fiye da mutane dubu 12 sun rasa matsaugunansu bayan da  ruwan ya haddasa ambaliya tare da  lalata kayayyakin more rayuwa da tsirrai.

Alkaluman da mahukuntar Angola suka bayar sun nunar da cewa ruwan ya latata majami'u 12 da gidaje 378 a jihohi 12 daga cikin 18 da kasar ta kunsa. Wannan ambaliyar ta kuma haddasa matsalar katsewar wutar lantarki da katsewar hanyoyin sadarwa. Sai dai ruwan sama ya zo ne bayan shekara guda na fari da aka jima ba a ga irinshi ba a Kudancin Angola, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da shanu dubu 30,000, a cewar hukumomin kasar.