1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Gaza na cikin mawuyacin hali

July 31, 2014

Hukumomar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu na korafin rashin kayayyakin agaji dan tallafawa masu gudun hijira sakamakon hare-haren Isra'ila a zirin Gaza

https://p.dw.com/p/1Cn6z
Gaza Menschen auf der Flucht durch die Straßen die meisten Opfer sind Kinder
Hoto: Reuters

Hare-haren da Israila ke kaiwa Zirin Gaza a wuni na 24 yanzu ya jefa rayuwar mutanen yankin cikin wani yanayin da ba a taba gani, abin da ya sanya wani mawakin cikin gida da ke wakiltar hukumar kulda da 'yan gudun hijrar Falasdinu, na Majalisar Dinkin Duniya yin kiran da a kawo musu dauki. Mohammed Assaf wanda ya taba lashe wata gasar wakoki ta larabawa da ake kira Arab Idol ya yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa kasarsa na haihuwa bayan da ya raka wani jirgin da ke dauke da kayayyakin agaji daga Dubai zuwa Jordan.

Haka nan kuma mai magana da yawun Hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu na Majalisar Dinkin Duniya a Gaza, Chris Gunness fashewa ya yi da kuka bayan da wata kafar yada labarai ta yi masa tambaya kan wasu mutane 16 da suka hallaka da tashin bam din da ya fada makarantar Majalisar Dinkin Duniyar da ke Gaza.

Hukumar dai ta ce yauni ya yi mata yawa yanzu kuma tana fama da karancin kayayyaki domin adadin wadanda ke bukatan abinci da magunguna ya wuce misali.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu