Al′ummar Gabon na zaben shugaban kasa | Labarai | DW | 27.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'ummar Gabon na zaben shugaban kasa

Yakin neman zabe dai ya fi zafi tsakanin wanda ake kallon masani a harkokin diplomasiya da ya rike hukumar tarayyar Afirka a baya Jean Ping da Shugaba Ali Bongo tsakanin 'yan takara biyu

Gabun - Präsident Ali Bongo Ondimba

Shugaba Ali Bongo Ondimba ya dai ci gaba da mulkin Gabon tun a 2009 bayan zabe

A ranar Asabar din nan ce al'ummar kasar Gabon ke fita dan kada kuri'ar zaben shugaban kasa. Zaben da ake ganin ko dai ya yi gaba da shugaba Ali Bongo ko kuwa ya ci gaba da rike ragamar mulkin kasar ta Gabon. Bayan da ya karbi mulkin kasar a zaben 2009 da ke zuwa bayan da mahaifinsa Omar Bongo rasu bayan ya kwashe shekaru 41 akan mulkin wannan kasa.

Yakin neman zabe dai ya fi zafi tsakanin 'yan takara biyu daga cikin goma wato tsakanin wanda ake kallon masani a harkokin diplomasiya da ya rike hukumar tarayyar Afirka a baya Jean Ping da Shugaba Ali Bongo wanda duka sun yi aiki karkashin Shugaba Omar Bango. Zaben dai na zuwa a daidai lokacin da al'ummar wannan kasa ta Gabon ke kokawa da matsi na tattalin arziki, abin da baya rasa nasaba da faduwar darajar albarkatun mai da kasar ke fitarwa zuwa kasuwannin waje.

Masu zabe 628,000 ne daga cikin al'ummar kasar miliyan daya da dubu dari takwas suka cancanci kada kuri'a, a wannan zabe da duk wanda ya samu rinjaye tun a karon farko zai kai ga shugabancin kasar.