1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka ta Kudu

Afirka ta Kudu: Ko jam'iyyar ANC za ta samu nasara?

Ngutjinazo, Okeri Abdulkarim
May 29, 2024

Kimanin mutane miliyan 28 ne suka yi tururruwar kada kuri'a a rumfunan zaben kasar Afirka ta Kudu a daidai lokacin da kasar ke cika sharu 30 cif da komawa kan tafarkin mulkin demokaradiyya

https://p.dw.com/p/4gQEE
Hoto: Zinyange Auntony/AFP

Shugaba mai ci  Cyril Ramaphosana cikin halin tsaka mai wuya, bayan da masana suka yi hasashen cewa ba lallai ne jam'iyyarsa ta ANC ta samu rinjaye a zaben ba, sakamakon taskun da kasar ta fada ciki na kangin rayuwa da fatara da talauci da aikata miyagun laifuka tsakanin al'umma, baya ga cin hanci da rashawa da ke zama babban dabaibayin da ke yi wa mulkinsa tarnaki.

 Ramaphosa ya bugi kirjin cewar za su samu nasara a zaben

 Cyril Ramaphosa
Cyril RamaphosaHoto: Oupa Nkosi/REUTERS

Ya ce''Wannan kyakkayawar rana ce mai matukar muhimmanci, kuma zabe yana tafiya daidai kamar yadda ya kamata a fadin kasar, hakika na ji dadin zuwa yankina da na girma a ciki,na gaisa da jama'a har da wakilan jam'iyyu da ke rumfar zabe. Kuma ina da kwarin gwiwar cewa al'ummar Afirka ta Kudu za su sake zabar jam'iyyarmu ta  ANC''.

Alkawarin farfado da tattalin arzikin Afirka ta Kudu daga ANC

Wahlen in Südafrika 2024
Hoto: PHILL MAGAKOE/AFP

Cyril Ramaphosa ya dare kan karagar mulkin ne a shekarar 2018, bayan sauke Jacob Zuma bisa aikata laifuka iri-iri, da suka hada da cin hanci da rashawa, halasta kudaden haram, kin biyan haraji da kuma almundahana. Mai shekaru 71, Mr Ramaphosa ya alkawarta farfado da komadar kasar, ko da yake masharhanta sun ce ya riga ya nuna gazawarsa a fili karara, sakamakon yadda rashin aiki yi a kasar ya kai kololuwar da ba taba gani ba a tarihi. Lamarin ya jefa ANC cikin yanayin fuskantar sakamakon zabe  mafi muni.

Julius Malema na neman ganin an samu sauyin mulki a Afirka ta Kudu

Julius Malema
Julius MalemaHoto: Guillem Sartorio/AFP

Shi kuwa jigo a cikin 'yan adawa Julius Malema mai shekaru 43, shi ne jagoran jam'iyyar Economic Freedom Fighters, EFF, da ya kafa a shekarar 2013, bayan korarsa da aka yi daga ANC sakamakon tayar da tarzoma, a lokacin yana rike da mukamin shugaban matasa na jam'iyyar. jam'iyyarsa ta samu karbuwa a kasar sakamakon manufofinta na bunkasa tattalin arzikin kasa da tabbatar da adaci da daidaito a rabon filaye ga 'yan kasa. Duk da kallon da ake masa na mai yayyafar siyasa da kuma janyo cece-kuce, Julius Malema na cikin wadanda masu hasashen ke cewa ka iya zama shugaban Afirka ta Kudu a  nan gaba.