Al′umma na kada kuri′a a Iran | Labarai | DW | 18.06.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'umma na kada kuri'a a Iran

Al'umma na kada kuri'a a Iran domin zaben sabon shugaban kasa da zai gaji  Hassan Rohani, mutane kusan miliyan sitin ne wadanda aka yi rijista za su kada kuri'a.

 Ebrahim Raisi dan takarar da ake tsamani zai samu nasara a zaben

Ebrahim Raisi dan takarar da ake tsamani zai samu nasara a zaben

'Yan takara hudu ne ke faffatawa a zaben bayan da uku suka janye wanda ake hasashen Ebrahim Raisi mai matsagaicin ra'ayi zai samu nasara. Jagoran addini  Ayatollah Ali Khamenei ya yi kira ga jama'ar kasar da su fito don kada kuri'a, wanda wasu suka yi fatali  da zaben saboda halin matsi na tattalin arziki da Kasar ta Iran take ciki.