Al′umar kasar Kuba sun yi fatan kyautatuwar rayuwa | Labarai | DW | 18.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'umar kasar Kuba sun yi fatan kyautatuwar rayuwa

Bayan sanarwar maido da hulda jakadanci tsakanin Kuba da Amirka, mazauna birnin Havana na Kuban sun yi fatan samun karin arziki da wadata.

Fatan samun zaman lafiya da ingantuwar matsayin rayuwa ya fito fili a kan titunan birnin Havana na kasar Kuba a wannan Alhamis bayan labarin nan mai cike da tarihi na maido da huldar diplomasiyya tsakanin Kuban da Amirka. Bayan watanni 18 na tattaunawa cikin sirri, shugaban Amirka Barack Obama da takwaransa na Kuba Raul Castro sun amince da wani shirin musayar firsinoni, da bude ofisoshin jakadanci a kasashensu tare kuma da saukaka takunkumin ciniki tsakani. Wani dan Kuba fatansa ya nuna kamar haka.

"Kuba na fatan samun karin arziki da wadata sakamakon wannan sabuwar huldar dangantaka. Babban albishir ne na karshen shekara. Tattalin arzikin kasarmu zai bunkasa, hulda za ta yi kyau bayan shekaru 56, wannan abu ne mafi alheri ga al'umarmu."