Alkalan Kwango na koyon darasi a Togo | Siyasa | DW | 09.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Alkalan Kwango na koyon darasi a Togo

Tawagar mambobin kotun tsarin mulkin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango na gudanar da wata ziyara a kasar Togo domin daukan darasi daga takwarorinsu na kasar ta Togo kan hanyoyin da suka bi a fannin dimokuradiyya.

Oberster Gerichtshof des Kongos weist Wahlbeschwerde Bembas zurück (picture-alliance/ dpa)

Wata tawagar mambobin kotun tsarin mulkin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango na gudanar da wata ziyara a kasar Togo domin daukan darasi daga takwarorinsu na kasar ta Togo kan hanyoyin da suka bi a fannin dimokuradiyya. Sai dai wasu na ganin lamarin a matsayin karkacece ganin yanayin siiyasar kasar ta Togo da ita ma ta ke fama da rikicin siyasa.

Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango dai ta fuskanci tarin matsaloli na siyasa da suka danganci gudanar da zabuka a kasar da sau tari ke kaiwa ga dage lokutan zabuka. A yanzu dai ta tabbata cewa zabukan gaba, za su gudana a shekara ta 2018. Hukumomin na Kinshasa dai za su tsunduma cikin wasu jerin sauye-sauye da 'yan kasar suka bukaci a samar, a saboda haka ne wannan tawaga ta mambobin kotun tsarin mulkin kasar ta Kwango ke ziyara a kasar Togo. 

Shugaban tawagar alkalan na Kwango, ya ce a shekara ta 2015 aka samaf da totun tsarin mulkin ta Kwango kuma tun daga wannan lokaci kokarin koyon darasi daga kasashe daban-daban. Suma dai masu lura da al'amuran siyasar kasa da kasa sun dubi lamarin a matsayin karkatacce domin kuwa a cewar Farfesa David Dosso Malami a jami'ar birnin Lome na kasar Togo, a kasar dai ba za a iya daukar misalin kwarai ba kan harkokin dimokuradiyya. Kamar yadda shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe ya gaji mahaifinsa a shekara ta 2015 ba bisa ka'ida ta dimokaradiyya ba, haka shi ma shugaba Joseph Kabila na Kwango da ke fuskantar bore daga al'ummar kasarsa, ya zo kan mulki a shekara ta 2001 inda ya gaji mahaifinsa da aka kashe.