Alkalan kasar Gabon sun shiga yajin aiki | Labarai | DW | 15.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alkalan kasar Gabon sun shiga yajin aiki

Kotunan Gabon sun kasance wayam saboda alkalai suka ce ba za su gudanar da shari'a ba matikar gwamnati ba ta tsige Ministan shari'a daga mukaminsa ba bisa zargin shisshigi a harkar shari'a.

Supreme Court of Appeal in Bloemfontien

Alkalan kasar Gabon sun shiga rana ta biyu na yajin aikin sai Baba ta gani da suka fara a ranar Alhamis da nufin ganin an tsige Ministan shari'a Francis Nkéa Ndzigue daga mukaminsa bayan da ya zargesu da cin hanci da karbar rashawa. Dama dai sun jima suna korafi kan shisshigin da bangaren mulki ke yi wa harkar shari'a a Gabon, lamarin da suka ce ba za su laminta ba saboda ya saba wa tsarin dimukaradiyya.

Shi dai Francis Nkéa Ndzigue ya fara takun-saka ne da alkalai bayan da a farkon watan Disemba wata kotu a Liberville ta wanke wani abokin gaban ministan shari'a da laifin da aka zargeshi da aikatawa. Sai dai ministan ya nemi a ladabtar da alkalin tare da dakatar da shi daga aiki.

Alkalan na Gabon sun yanke shawarar maka ministan shari'a kasarsu a kotu saboda bata musu suna da shisshigi da yake musu. Har yanzu fadar mulki ta Libreville bata bayyana matsayinta a kan wannan batu ba.