1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alkalan kotun koli byu sun mutu a Afghanistan

Abdoulaye Mamane Amadou
January 17, 2021

Wasu mata alkalan babbar kotun kolin birnin Kabul biyu sun mutu a yayin wani harin da 'yan bindiga suka kai kan motarsu a daidai lokacin da suke hanyar zuwa aiki.

https://p.dw.com/p/3o1nJ
Afghanistan Kabul Bombenanschlag
Hoto: Rahmat Gul/AP/picture alliance

Da sanyin safiyar yau ne maharan dauke manyan bindigogi, suka saita matan alkalan kotun kolin kasar, kuma suka bindige su a harin tare da jikkata drebansu, a cewar kakakin kotun kolin Ahmad Fahim Qaweem.

Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da babban birnin Khabul na Afghanistan ke fama da jerin hare-haren ta'addancin da ake zargin kungiyar Taliban ce ke kai su.

Bisa shiga tsakanin Amirka, har yanzu ana samun jan kafa wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnati da 'yan Taliban don tabbatar da zaman lafiya a kasar, yarjejeniyar da ta ba wa Amirkar damar soma janye dakarunta da ke kasar.