1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Miliyoyi za su shiga macin adawa da Shugaba Bouteflika

Ramatu Garba Baba
March 8, 2019

Manyan 'yan siyasa na jam'iyyar FLN mai mulkin Aljeriya da dama sun yi murabus tare da shiga gangamin da aka shirya gudanarwa a wannan Juma'a don nuna adawa da yunkurin sake tsayawa takara na Shugaba Bouteflika.

https://p.dw.com/p/3Efuj
Algerien Algier - Proteste gegen Abdelaziz Bouteflika gegen weitere Amtszeit
Hoto: Imago/Xinhua

Albarkacin wannan gangamin, an dakatar da duk wata zirga-zirga na layin dogo a duk fadin Algiers babban birnin kasar. 'Yan adawa sun yi wa gangamin lakabi da macin mutum miliyan ashirin. Sun kuma ce zai kasance irinsa na farko a tarihin kasar. 

Shugaban mai shekaru tamanin da biyu da haihuwa, ya kwashi fiye da shekaru ashirin ya na mulki amman jama'a sun soma baiyana rashin gamsuwarsu bayan da ya shafe shekaru yana fama da rashin lafiya wanda a dalilin hakan baya ma iya fitowa bainar jama'a. Sai dai a wata sanarwa da Shugaban ya fitar a jiya Alhamis, ya gargadi masu zanga-zangar da su gujewa duk wani lamari da ka iya jefa kasa cikin rudani.

Tun shekarar 2013 rabon da Shugaba Bouteflika ya yi wa jama'rsa bayani kai tsaye.a gabanin gagarumin gangamin da jama'a suka shirya don hana Shugaba Abdel-aziz Bouteflika sake tsayawa takara a zaben kasar mai zuwa.