1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aljeriya: Muhawara kan murabus din Bouteflika

Mahmud Yaya Azare GAT
April 2, 2019

A Aljeriya, ana ci gaba da mayar da martani kan sanarwar da fadar gwamnatin kasar ta yi kan cewa, Shugaba Abdel Aziz Bouteflika zai yi murabus kafin ranar 28 ga watan Afrilu na wannan shekara.

https://p.dw.com/p/3G6FF
Algerien, Algier:  Algerisches Militär fordert Absetzung von Präsident Bouteflika
Shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz BouteflikaHoto: picture alliance/dpa

Wata sanarwa daga ofishin shugaban kasar ta ce kafin shugaban dan shekaru 82 wanda ya yi shekaru 20 kan mulki, bai dauki matakin yin murabus a karshen wa,adin mulkinsa da ke karewa ran 28 ga wannann watan, sai da ya tabbatar ya dauki matakan hana samun tseko wajen gudanar da ayyukan gwamnatin kasar, ta hanyar yin garambawul a gwamnati, inda aka sauke tsofin fiskoki da nada wasu sabbi, matakin da amma wasu 'yan adawa ke wa kallon azarbabiya ce irin ta shugaban:


"A dokance shugaban nan mulkinsa na karewa ne ran 28 ga watan Maris, don haka duk wasu nade-nade da garambawul da shugaban zai yi, tamkar yana neman sai ya kakaba wa mutane mukarrabansa ne duk da shi zai sauka. 'Yan kasa kuma sun riga sun nuna ba sa son irin wannan kwan gaba-kwan bayan irin na 'yan siyasa.”


Duk da hakan dai, da dama daga 'yan kasar sun yi murna da wanna mataki da suke ganin tamkar nasarar ce ga zanga-zangar da suka kwashe kusan makwanni shida suna yi, duk da cewa suna ganin har yanzu ba a rabu da Bukar ba:

Algerien, Algier: Proteste gegen Algeriens Staatschef
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Batiche


 “Ka karasa hidimta wa 'yan kasar da kake kafin wannan wa,adin naka ya kare. Ka yi abun da za,a tina da alheri a bayanka. Ka aiwatar da sauran ayoyin dokar da za su ba wa 'yan kasa 'yanci zaba wa kansu shuwagabanni. Lalle ya kamata ka saurari wannan kiran.”


 Galibin 'yan kasar dai sun yi amannar cewa, muddin ba sabon zibi aka yi aka kawar da mukarraban Boutifilika da suka yi kaurin suna wajen shirya magudin zabe ba, to tamkar an yi aikin baban giwa ne:

Abdelaziz Bouteflika, Präsident Algerien
Hoto: picture-alliance/K. Mohamed


“Abun da ke wakana yanzu wasu za su iya daukarsa nasara ce ga fafutukar neman sauyi. Amma a gaskiya, har yanzu masu zanga-zanga na ganin ba a rabu da Bukar ba, muddin dai ba a kafa gwamnatin rikon kwaryar da jama,a za su nutsu da ita kan cewa za ta jagoranci shirya zabe mai tsafta ba.”


Wasu dai na ganin matakin sanya sabin fuska a gwamnatin rikon kwaryar da Boutafilikan ya dauka, da kame wasu mukarrabansa da ake tuhuma da badakala, gami da hana tashi da saukar jirage masu zaman kansu a kasar, duk wadannan matkai ne da Boutafilikan ke yi,don nunawa 'yan kasar da ke matukar kishirwar samun sauyi na hakika, kan cewa da gaske yake, ya ga ya biya musu bukatunsu.