Aljeriya: Daure matashi dan fafutika | Labarai | DW | 23.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aljeriya: Daure matashi dan fafutika

Wata kotu a Aljeriya ta yanke hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari ga matashin nan shugaban wasu hadin gwiwar kungiyoyin matasa da ake kira (RAJ) bisa tuhumarsa da yin bore da zanga-zanga.

Lauyan da ke kare matashin ya bayyana shafinsa na Facebook a yau Litinin da cewa alkali mai shigar da kara ya yanke hukuncin zaman gidan waklafin ne na shekaru biyu a yayin wani zama a asirce da kotun ta gudanar a birnin Algers, sai dai lauyan ya ce za a yi gundarin zaman shari'ar ne a ranar shida ga watan gobe.

Wannan hukuncin kotun na zuwa ne a daidai lokacin da ma'aikatar shari'ar kasar ta bayyana dage sauraren duk wata kara a cikin kotunan kasar har ya zuwa 31 ga wanann watan da muke ciki.