Alhinin kasashen duniya ga Jamus | Labarai | DW | 16.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alhinin kasashen duniya ga Jamus

Shugabanin kasashen duniya na ci gaba da nuna alhini dangane da mutuwar tsohon shugaban gwamnatin Jamus Helmut Kohl wanda ya rasu a yau juma'a yana da shekaru 87.

Shugabar gwamnatin Jamus  Angela Merkel a sakonta na ta'aziyya, ta ce Helmut Kohl ya bayyana a dai dai lokacin da guguwar sauyi ta kada a yankin Turai, Merkel ta kuma jinjinawa Kohl kan rawar da ya taka wajen hada kan 'yan kasar.

A daya bangaren,  Martin Schulz na jama'iyar adawa ta SDP a kasar ya ce duk da bambancin ra'ayin siyasa ya zaman masa dole ya jinjinawa tsohon shugaban bisa nasarorin da ya samu a kokarinsa na ciyar da Jamus gaba.

A nasa bangaren kuwa, Firaiministan Isra'ila  Benjamin Netanyahu ya ce mutuwar Helmut Kohl na nufin Isra'ila ta yi rashin babban aboki, ya kuma jajantawa al'umar kasar da kuma iyalan marigayin

a sakonsa na ta'aziya.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da tsohon shugaban Amurka George W Bush da kuma shugaban kungiyar tarrayar Turai Jean Claude Junker na daga cikin wadanda suka aika da sakon ta'aziyarsu.

Helmut  Kohl  ya ja ragamar shugabancin Jamus har tsawon shekaru 16, kuma hakan ya sa ya kasance shugaban da ya fi dadewa bisa mulki tun bayan yakin Duniya. Ana kuma tuna shi bisa rawar da ya taka wajen hada kan yan kasar da kuma kokarinsa na ganin Jamus ta amince da amfani da takardar kudi ta bai daya da Turai.

Marigayi Helmut Kohl, ya rasu ne a wannan Juma'ar, bayan fama da jinya sakamakon wata faduwar da ya yi tun a cikin shekara 2008.