Al′amura sun fara komawa daidai a Gabon | Labarai | DW | 02.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'amura sun fara komawa daidai a Gabon

Mahukuntan kasar Gabon sun baza sojoji a Libreville babban birnin kasar, yayin da al'ummar kasar suka fito domin sayen kayan masarufi bayan zanga-zangar adawa da sakamakon zabe.

Al'amura na dai-daita a Gabon bayan zanga-zanga kan sakamkon zabe

Al'amura na dai-daita a Gabon bayan zanga-zanga kan sakamkon zabe

Zanga-zangar dai ta biyo bayan ayyana shugaban kasar mai ci a yanzu Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben da hukumar zaben kasar ta yi. Zanga-zangar ta tsahon yini biyu dai, ta yi sanadiyyar asarar rayuka uku yayin da kuma aka cafke wasu mutane akalla 1,100, magoya bayan dan takarar jam'iyyar adawa Jean Ping biyo bayan abin da jami'an tsaron kasar suka bayyana da kokarin far musu da suka yi. Sai dai duk da cewa wasu shaguna sun bude domin ci gaba da hada-hada, al'ummar kasar na fargabar cewa akwai yi wuwar dawowar tarzomar.