1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabin ministocin Masar sun kama aiki

Ahmed Salisu
June 14, 2018

Shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sissi ya rantsar da sabuwar majalisar ministocinsa mai mambobi 32 wadda Mostafa Madbouli zai jagoranta.

https://p.dw.com/p/2zYZ1
Ägyptens Präsident al-Sisi für zweite Amtszeit vereidigt
Hoto: picture-alliance/Xinhua/MENA

Majalisar ta kunshi sabbin ministoci da kuma wanda ya yi aiki da su a gwamnatin baya. Sabbin ministocin sun hada da wanda zai yi aiki a ma'aikatar kudin kasar da ta sufurin jiragen sama da kuma lafiya da muhalli. Yayin jawabinsa ga al'ummar kasar bayan da ministocin suka sha rantsuwar kama aiki, al-Sissi ya ce sabuwar gwamnatin za ta yi aiki wajen yin gyare-gyare na tattalin arziki inda za su fara da janye tallafi kan albarkatun man fetur wanda da dama ke ganin zai kara ta'azzara tsadar farashin kayayyaki a kasar.