Al Shabab ta hallaka sojoji 24 na AU | Labarai | DW | 30.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al Shabab ta hallaka sojoji 24 na AU

Kungiyar al Shabab a Somaliya ta yiwa tawagar sojin kungiyar tarayyar Afirka kwantar bauna wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojojin da dama.

Arangama a tsakanin Mayakan kungiyar al-Shabab a Somaliya da tawagar rundunar sojin kungiyar kasashen Afirka wato AU ta yi sanadiyar rayuka 24 ciki har dana maharan,

Mayakan sun far ma tawagar a kusa da garin Bulo-Marer kamar yadda wani babban jami'in sojin kasar ta Somaliya ya tabbatar ma manema labarai, harin na yau Lahadi na zuwa ne 'yan sa'oi kadan bayan kai harin kunar bakin wake da aka yi anfani da wata karamar mota a Mogadishu babban birnin kasar, mutane biyar ne suka mutu a harin kuma dukkaninsu fararren hula ne.

Kungiyar  Al-Shabab ta dauki alhakin kai harin inda ta ce ta kashe sojoji 39