al-Shabab sun kashe mutane 12 a Kenya | Labarai | DW | 25.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

al-Shabab sun kashe mutane 12 a Kenya

A kalla mutane 12 ne suka mutu a wani harin bam da ake zargin 'yan ta'addan Somaliya suka kaddamar a garin Mandera da ke arewa maso gabashin kasar Kenya.

'Yan sanda da ke yankin Mandera a kan iyaka da kasar Somaliya sun tabbatar da aukuwar harin sun ce suna zargin mayakan kungiyar al-Shabab na kasar Somaliya ne da kaddamar da harin da ya yi sanadiyar rayukan fararen hula. Hukumomin 'yan sandasun ce maharan sun zo da manyan makamai sannan suka tashi bam a wani gidan saukan baki na Bishoro inda kusocin gwamnati ke sauka.

Babu dai martani daga kungiyar ta al-Shabab da ake zargi da kai wannan hari, to amma kungiyar ta sha alwashin ci gaba da kai kai hare-hare mai kama da ramuwar gayya da daukar fansa a kasar kenya tun bayan da gwamnatin Kenya ta jibge jami'an tsaronta a Somaliya da nufin murkushe ayyukan ta'addanci kungiyar al-Shabab.