Al-Shabaab ta musanta kashe ′ya′yanta | Labarai | DW | 12.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-Shabaab ta musanta kashe 'ya'yanta

Kungiyar al-Shabaab a kasar Somaliya, ta musanta ikirarin da wata rundunar da Amirka ke jagoranta ta yi na kisar 'ya 'yan kungiyar a wani farmaki da ta kaddamar ta sama a kasar.

Sheikh Abdiasisi Abu Mus'ab da ke zaman wani kusa a kungiyar ta al-Shabaab ne ya musanta ikirarin, inda kuma ya zargi gwamantin Somaliya da zuki-ta-malle kan harin da aka ce an kaddamar kan kungiyar a babbar tungarsu da ke Jilib a Kudu da Mogadishu babban birnin kasar. A wannan Asbara din ne gwamnatin kasar Somaliyar ta sanar da nasarar halaka mayakan na al-shabaab 81. Ita ma Amirka a ranar Alhamis ta sanar da kai wani farmaki kan kungiyar. Cacar baka kan nasarorin kaddamar da hare-hare tsakanin gwamnatin Somaliya da bangaren na al-Shabaab dai ba sabon abu bane, inda galibi ake gaza iya tantance hakikanin gaskiyar lamarin.