1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Shabaab ta yi ikirarin kai harin Nairobi

Gazali Abdou Tasawa MNA
January 15, 2019

Kungiyar Al-Shabaab mai da'awar jihadi a Kenya ta dauki alhakin kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar a wannan Talata a birnin Nairobi.

https://p.dw.com/p/3Bbkl
Kenia Angriff auf Hotel in Nairobi
Hoto: Getty Images/AFP/S. Maina

A kasar Kenya kungiyar masu da'awar jihadi ta Al-Shabaab ta dauki alhakin harin da aka kai a wannan Talata a birnin Nairobi, inda bayan da maharan suka tayar da bam a wani waje mai tarin shaguna da ofisoshin gwamnati, suka kuma buda wuta da bindigogi kan jama'a. 

A cikin wani gajeran sako da ta wallafa a kafar farfagandarta ta Shahada, ta ce wasu mayakanta ne suka kai harin. Sojojin rundunar yaki da ayyukan ta'addanci ta kasar a cikin motoci masu sulke da ma jami'an kashe gobara sun kawo dauki ga mutanen da lamarin ya rutsa da su. 

Daga nasu bangare jami'an kwance bama-bamai sun yi nasarar tayar da wani bam din da aka dana a kan motar da maharan suka yi amfani da ita wajen kawo harin. Mahukuntan kasar dai sun tabbatar da mutuwar akalla mutane biyar a cikin harin.