Al Qaeda ta karbe wasu garuruwa a Yemen | Labarai | DW | 02.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al Qaeda ta karbe wasu garuruwa a Yemen

Rahotannin daga kasar Yemen na cewar 'yan kungiyar Al Qaeda sun karbe iko da garuruwan Zinjibar da Jaar da ke da muhimmanci a kudancin kasar.

Mazauna yankunan da suka tabbatar da wannan labarin sun ce 'yan kungiyar ta Al Qaeda sun kai ga kame garuruwan ne bayan da suka kai wasu jerin hare-hare inda suka yi taho mu gama da wasu mayakan sa kai a yanki.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce yanzu haka mayakan Al Qaeda din sun sanya shigaye kan manyan hanyoyi na shiga garuruwa kuma bayan kammala sallar Asubahin wannan Larabar suka yi shelar maida su karkashin ikonsu.