Al-Ka′ida ta kai hari a Burkina Faso | Labarai | DW | 28.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al-Ka'ida ta kai hari a Burkina Faso

Kungiyar 'yan ta'addan ta dauki alhakin harin da aka kai kan ofisoshin 'yan sanda biyu a birnin Ouagadougu na kasar Burkina Faso. Hukumomi sun ce maharan sun yi awon gaba da kadarori da dama.

Kawo yanzu babu rahotannin asarar rai daga harin, sai dai an samu jikkatar wata jami'ar 'yan sanda. Wannan harin dai na zuwa ne a dai dai lokacin da birnin na Ouagadougou ke cike tsauraran matakan tsaro, ganin manyan baki na halartar bikin baje kolin fina-finan Afirka. Kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai, na ci gaba da zama barazana ga kasar Burkina Faso, inda ake yawaita kai hare-hare da yin garkuwa da mutane. A watan Disemban da ta gabata kungiyar Ansarul Islam, ta yi ikirarin kai harin da ya hallaka dakarun soji 12 a kan iyakar kasar da Mali. A yanzu dai hukumomin kasar na ci gaba da zurfafa bincike dan gano mabuyar mayakan.