Air Berlin ya rufe harkar jigila | Labarai | DW | 28.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Air Berlin ya rufe harkar jigila

A daren da ya Juma'a ne jirgin karshe na Air Berlin, ya sauka a cibiyarsa da ke Tegel, wanda ya tabbatar da kawo kitse harkokin kamfanin da ya yi kusan shekaru 40 yana sufurin sama.

A daren da ya gabata ne jirgin karshe na Air Berlin, ya sauka a cibiyarsa da ke Tegel, wanda ya tabbatar da kawo kitse harkokin kamfanin da ya yi kusan shekaru 40 yana sufurin sama. Kamfanin surufin jiragen nan mai saukin kudi a Birtaniya wato Easy Jet, shi ne ya sayi wani bangare na kamfanin na Air Berlin na Jamus, wanda ya shiga garari. Cinikin da ya kai na euro miliyan 40, ya shafi manyan jirage 25 ne sanfurin A320.

Bayan wannan cinikin dai kamfanin na easy jet na kasar Birtaniya, ya amince zai dauki matuka da masu hidima cikin jiragen kamfanin na Air Berlin kimanin dubu guda, wadanda zai dauke su bisa tsari na kwantargi.  Air Berlin wanda ke matsayi na biyu a jerin kamfanonin jirage a Jamus yana da ma'aikata akalla 8000. Ya dai shiga garari ne cikin watan Agustan bana, bayan tsame hannunsa da babban mai hannun jari a cikinsa wato kamfanin Etihad na hadaddiyar daular larabawa, ya yi.