Aikin Uranium ya gurbata ruwa a garin Arlit | Zamantakewa | DW | 25.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Aikin Uranium ya gurbata ruwa a garin Arlit

Rayuwar al'umma mazauna Arlit dake arewacin Nijar da ma yanayin yankin na cikin mawuyacin hali sakamakon aikin kamfanonin hakan ma'adinan karkashin kasa.

Fiye da shekaru 10 kenan da kungiyoyin fara hula na garin Arlit ke fitowa suna kokowa don ganin an inganta rayuwar al'umma da ke zaune a garin wanda ke dauke da kamfanonin hako ma'adinai na karfen Uranium wanda aikin tonon shi ya kawo illoli da dama ga rayuwar al'umma da kuma yanayi. daga ciki akoye gurbatar wuraren kiwo noma ruwan cha , da sauran su.a kan haka nema alouma da kungiyoyin fara hula suka yi zagayen gani da ido cikin garin na Arlit don ganin irin halin da al'umm ke ciki.

Zagayen gani da ido a cikin garin dai ya hada 'yan jarida da kungiyoyin fara hula da al'umma ya fahimtar da 'yan jarida abubuwa da dama musamman ma matsalolin da aikin tonon karfen Uranium ke haifar wa garin na Arlit da ke nisan kilomita 263 daga arewacin Nijar wanda kuma arzikin garin ya ta'allaka ga kiwo, noma da kuma arzikin ma'adinai. Sai dai ayyukan kamfanonin sun kawo sauyin yanayi a bangaren rayuwar al'umma, misali gurbatar wuraren kiwo, noma, muhalli da ruwan sha.

Damuwar al'umma saboda rashin kulawa

Mafi yawan al'umma da ke zauna a garin na Arlit na nuna damuwa sosai ga panin kiwon lafiya musumen ire iren cututukan da ke adabar su , ga karamcin ruwan sha wanda watarana su kan gamu da ruwa marasa kyau to ko kaka ne kungiyoyin fara fula ke kalon wanan lamarin Ahmed Wagaya yayi tsokaci kan batun yana mai cewa abin ya wuce misali.

Bincike dai ya nuna cewa mutanen da ke zaune a garin Arlit da ma kewaye su suka fi fuskantar barazana daga illolin da aikin na tonon uranium ke haifarwa , to ko wane irin kokari gwamnatin kasar Niger ya kamata tayi don ganin talakawan garin Arlit sun amfana da tsabtatattun ruwan sha kuma.

Kungiyoyin fara hula da ma alouma a garin na arlit kokowar su ta farko, ita ce samar da ruwan sha tsabtatattu kuma wadatattu, inganta wuraren kiwo tare da samar da magunguna isassu a asibitoci na gwamnati.

Mawallafiya: Tilla Amadou
Edita: Mohammad Nasiru Awal