Aikin tsabtace Ogoni zai ci dala biliyan guda | Siyasa | DW | 02.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Aikin tsabtace Ogoni zai ci dala biliyan guda

Sakamakon mai da ya malala a Ogoni da ke jihar Rivers a yankin Niger Delta, gwamnati ta dauki alkawarin kashe makuddan kudi wajen share dagolon man.

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, ya kaddamar da shirin tsabtace yankin na Ogoni wan zai ci kimanin dala biliyan daya, bayan da Shugaba Buhari ya soke ziyararsa a wannan yanki da ke fama da rigingimun masu tada kayar baya.

Yemi Osinbajo dai ya wakilci Buhari, wanda ya kamata ya kaddamar da shirin na yankin Ogoni da ke jihar rivers, wanda da zai kasance ziyararsa ta farko zuwa yankin na Niger Delta a matsayin shugaban kasa.

mataimakin shugaban kasar ya ce, a shirye gwamnati take wajen tabbatar da adalci ga mutanen wannan yanki da suka dade cikin hali mawuyaci na gurbatar muhalli da rashin morar arzikin da yake yankinsu.

Babu dai wata sanarwa data biyo bayan soke ziyarar ta shugaban Najeriya zuwa kudancin kasar mai arzikin man petur, ziyarar da ke zuwa adaidai lokacin da hare haren mayu tayar da kayar baya ke kara ta'azzara.

Tuni dai Buhari ya bada umurnin tsaurara matakan tsaro a yankunan da ke da albarkatun mai, a yayin da sojojin kasar suka kira tsagerun Niger Delta Avengers, 'yan ta'addan tattalin arziki.

Sauti da bidiyo akan labarin