Binciken baraguzai bayan girgizar kasa
October 31, 2020Talla
Girgizar kasar wadda ta auku a jiya Juma'a ta yi sanadiyar mutuwar mutane 26 wasu da dama kuma suka jikkata. Girgizar kasar mai karfin maki bakwai a ma'aunin Richter ta haifar da tashin igiyar ruwan tsunami a yankin tsibirin Samos wanda ya janyo ambaliyar ruwa a gabar kogi a yammacin Turkiyya.
An jiwo amon girgizar kasar a cikin birnin Istanbul da kuma Athens. Girgizar kasar dai ta bude kofar tattaunawa ta diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu da ke takun saka a kwanakin nan.
Tuni Firaministan Girka ya kira shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ta wayar tarho domin yi masa jaje da kuma ta'aziyya.