Aikin ceto a Makkah bayan rushewar wani otel | Labarai | DW | 06.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aikin ceto a Makkah bayan rushewar wani otel

Masu aikin ceto a Saudiya na ci-gaba da aiki don ceto wadanda watakila ke da sauran numfashi a karkashin wani otel da ya rushe jiya a birnin Makkah. Ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 20 yayin da 59 suka samu raunuka sakamakon ruftawar otel din dake kusa da Kabah a daidai lokacin da ake dab da gudanar da aikin hajji na bana. Daga cikin wadanda wannan hadari ya rutsa da su akwai ´yan kasar Masar, Tunisia da Hadaddiyar Daular Labarawa sai kuma ´yan kasar Indonesia. A bana ana sa rai mutane miliyan 2.5 zasu yi aikin hajji a kasa mai tsarki.