Agaji na isa Yemen bayan tsagaita wuta | Labarai | DW | 13.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Agaji na isa Yemen bayan tsagaita wuta

Mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da bangarorin da ke fada da juna suka yi a Yemen ya bada damar fara Kai kayan agaji a sassa daban daban na kasar.

Kayan agajin gaggawa sun fara isa Yemen sakamakon mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta kwanaki biyar, da aka cimma tsakannin saudiyya da 'yan tawayen Huthi 'yan shia. Wata majiya mai tushe ta bayyana wa kanfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, wani jirgin ruwa mallakin Hukumar Abinci ta Duniya ya fara rabon barguna da tantuna da kuma abinci a larduna daban daban na kasar ta Yemen.

A nasa bangaren Sarki Salman na saudiyya ya bayyana cewar ya ninka kudin miliyan 544 na Dollar da kasarsa ta ware domin agaza ma wadanda rikici ya daidaita a Yemen.Yarjejeniyar tsagaita buden wutar ta bada damar kai kayan agaji zuwa ga wasu dubban jama'ar da yakin ya rutsa da su. Sai dai saudiyya da Kawayenta sun yi gargadin cewa za su mayar da martanni idan har 'yan tawayen na Huthi ba su mutunta yarjejeniyar ba.