1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Afirka ta Tsakiya ta amince da kudin Bitcoin

May 6, 2022

Afirka ta Tsakiya ta amince da soma amfani da kudin Bitcoin duk da fargabar da wasu a kasar ke nunawa kan hadari da ake gani a game da kudin a duniya.

https://p.dw.com/p/4AwG8
Bitcoin mit Doillarscheinen
Hoto: Marvin Samuel/TOLENTINO-PINEDA/Zoonar/picture alliance

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ce kasa ta farko a yankin Tsakiyar Afirkada ta amince da fara amfani da kudin Intanet na Bitcoin a hukumance. Majalisar dokokin kasar ta amince da kudin na Bitcoin cikin gaggawa duk da fargabar da wasu a kasar ke nunawa game da rashin tabbas a bangaren hadari da ake gani a game da kudin a duniya.

Zentralafrikanische Republik Parteitreffen mit Präsident Touadera
Shugaba Faustin Touadera na Afirka ta TsakiyaHoto: DW/J. M. Bares

Gwamnatin Shugaba Faustin Touadera wadda ta amince da amfani da kudaden Intanet din a hukumance a matsayin kudin kasa, ta ce tana da yakinin shigo da kudin a tsarin hada-hada ta kasar da zai inganta rayuwar al’umma.


Haka ma yin hakan a cewar gwamnatin zai sanya kasar cikin jerin kasashen da suka yi kukan kura a taswirar duniya wajen amincewa da kudaden na Bitcoin duk da dari-dari da ake yi da su. Masharhanta kan lamuran siyasa da masana harkokin kudade na ci gaba da gargadi kan gaggawar amince da kudaden a kasa, inda suke cewa ba zai taba iya warware matsalolin kasa-da-kasa ba.

Bitcoin
Afirka ta Tsakiya ce kasa ta farko da ta soma amfani da Bitcoin a AfirkaHoto: picture-alliance/empics/D. Lipinski

 Duk da arzikin zinare da lu’u-Lu’u da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke da shi, kasar na ci gaba da zama cikin jerin kasashe matalauta a duniya, da kuma ke fama da rikice-rikice na tsawon shekaru.

A yanzu kasar na amfani ne da kudaden CFA da Faransa da ta rene ta ta bar mata. Wasu na ganin amincewa da Bitcoin da kasar ta yi, a matsayin wani kokarin da kasar Rasha ke yi na rusa darajar kudin na CFA  na Faransa, domin ta samu iko da tattalin arzikin kasar.
Darajar kudaden na Bitcoin a bara ta yi wani irin tashi da ya kamar kashi 150%, da ya kai na miliyoyin dala. Sai dai kuma sun sake faduwa a watannin baya-bayan nan daga bayanan alkaluman hada-hada na ranar Larabar da ta gabata.