1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu ta caccaki Trump

August 24, 2018

Hukumomin Afirka ta Kudu sun zargi shugaban kasar Amirka da yin kalaman tunzura rigimar wariyar launin fata.

https://p.dw.com/p/33flE
Südafrika Präsident Cyril Ramaphosa im Parlament
Hoto: Getty Images/AFP/R. Bosch

Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta zargi shugaban Amirka Donald Trump da rura wutar rikicin wariyar launin fata, bayan wasu kalaman da ya yi kan filayen noma a kasar.

Cikin wani sakon twitter da Mr. Trump din ya wallafa, ya ce hukumomin Afirka ta Kudun na kwace filayen noma daga farar fatar kasar tare ma da kashe wasu daga cikinsu.

Sai dai gwamnati ta ce bata ji dadin kalaman na shugaban na Amirka ba, saboda babbar magana ce da ke iya raba kasar da a baya ta fuskanci wariyar launin fata.

Tuni dai ma'aikatar harkokin wajen Afirka ta Kudu, ta yi magana da jami'an jakadancin Amirka da ke kasar, inda ta wofintar da zancen da ta ce siyasa ce kawai.

Ita ma ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce za ta nuna bacin ran kasar ta hanyar tuntubar takwararta ta Amirka.