1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin aikin yi a Afirka ta Kudu

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 3, 2019

Rahotanni daga Afirka ta Kudu na nuni da cewa tattalin arzikin kasar ya samu koma baya a zango na uku na wannan shekarar.

https://p.dw.com/p/3U9Ig
Südafrika Pretoria Proteste
Matsalar rashin aikin yi, ta janyo zanga-zanga a Afirka ta Kudu.Hoto: picture-alliance/abaca/C. Tukiri

Hukumar kididdiga ta Afirka ta Kudun ce ta bayyana hakan, abin da ya saba da bayanan da ke nuni da cewa tattalin arzikin kasar ya farfado a zango na biyu na wannan shekarar, da aka ce ya taimaka wajen tsamo kasar daga masassarar tattalin arzikin da take ciki. A wata sanarwa da hukumar kididdigar ta Afirka ta Kudu ta fitar, ya nunar da cewa baki dayan karfin tattalin arzikin kasar ya ja da baya da digo shida cikin 100 yayin da ayyukan gona da hakar ma'adinai suka samu koma baya da sama da kaso shida cikin 100 kana masana'antun kasar suka rage yawan abin da suke fitarwa da kusan kaso hudu cikin 100. Har kawo yanzu dai Afirka ta Kudu ta gaza fitowa daga masassarar tattalin arzikin da duniya ta shiga tun a shekara ta 2008, sakamakon karuwar bashin da ake binta da matsalar tattalin arziki baya ga karuwar rashin aikin yi a kasar.