Afirka ta Kudu: An kame ′yan kasashen waje | Labarai | DW | 16.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afirka ta Kudu: An kame 'yan kasashen waje

Jami'an tsaro a Afirka ta Kudu sun cafke wasu 'yan kasashen ketare da yawansu ya kai 180, sakamakon kutsen da suka yi harabar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Pretoria.

Tun da farko daruruwan masu neman mafaka sun afka harabar cibiyar ne da nufin cigaba da wani zaman dirshan din da suka fara tun ranar 8 ga watan Oktoban da ya gabata, inda suka bukaci cibiyar ta mayar dasu wasu kasashen don tsira da rayukan su, biyo bayan rikicin kyamar bakin da ya afku a kasar a watan Satumba inda batagari a Afrika ta Kudu suka dinga kisa da kone baki tare da washe musu dukiyoyi.

A ranar Juma'ar da ta gabata  hukumar 'yan gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Dunya a Afirka ta Kudu ta bayyana cewar ba za ta tuhumi 'yan kasashen ketare da laifin cin zarafin wani jagoran addinin Kirista a cocin Cape Town ba, kasancewar 'yan kasashen ketaren na zaune ne a cocin da yake shugabanta saboda tserewa daga farmakin masu kyamar baki, duk kuwa da cewa Afirka ta Kudu na alfaharin samarwa baki shaidar zama a kasar tare da ayyukan yi cikin sauki.